Tattalin arzikin kasashen Tarayyar Turai ya ragu

Tattalin arzikin kasashen Tarayyar Turai ya ragu

An sanar da cewa sakamakon kwayar cutar Corona tattalin arzikin Nahiyar Turai ya ragu da kusan kaso 11.9 cikin dari a kashi na biyun watanni ukun shekarar bana idan aka kwatanta dana bara.

Hukumar Kididdigar Tarayyar Turai  (Eurostat), ta fitar da alkaluman bunkasar tattalin arzikin Tarayyar da yankunan dake amfani da kudin Euro.

Akan haka a yankunan masu amfani da Euro mai mambobi 19 an sama raguwar kudaden shiga da kaso 12.1 cikin dari a watani ukun kashi na biyun shekarar 2020 idan aka kwatanta dana bara.

Haka kuma a wannan lokacin kudaden shigar yankin ya ragu da kaso 15 a shekarar 2019.

Kasashen da suka samu raguwar kudaden shigar sun hada da Spain da kaso 18.5 cikin dari, Faransa kaso 13.8 cikin dari, Italiya kaso kao 12.4, Jamus kaso 10.1, Beljiyom kaso 12.2, Australia kaso 10.7, Portugal da kaso 14.1 cikin dari.

 


News Source:   ()