Tasirin jirage marasa matukan Turkiyya a fadin duniya

Tasirin jirage marasa matukan Turkiyya a fadin duniya

Yarjejeniyar da Turkiyya da Poland suka ratabawa hannu na siyar jirage marasa matuka kirar TB2 har guda 24 sun sake janyo hankali akan Turkiyya. Wadanan jiragen tsaron kirar TB2 ta kasar Turkiyya da aka siyar ga kasashen Katar, Libiya da Yukiren a kwanakin baya, wannan ne karon farko da wata mambar kungiyar NATO kuma mambar Tarayyar Turai za ta sayesu. Wadanan jirage marasa matuka kirar kasar Turkiyya dake cigaba da jawo hankula a kasar Turkiyya, akwai dalilai da dama da suka sanya Poland yanke hukuncin sayensu.

 

Akan wannan maudu’in mun sake kasancewa tare da Ferfesa Murat Yesiltas Daraktan Harkokin Tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato  SETA…

 

Da farko dai, kasancewar yadda kasar Turkiyya ta yi amfani dasu cikin nasara, ya sanya jiragen marasa matukan samun karbuwa a matakin kasa da kasa. Wadannan dai su ne jiragen marasa matukan da Turkiyya ke samarwa wadanda akayi wa lakabi da IHA da SIHA. Kasancewar yadda suka yi nasara a Siriya, Libiya da kuma ma a baya bayanan a Nagorno Karabakh musanman ma kirar Bayraktar TB2 ya sanyasu samun tagomashi a fadin duniya. Haka kuma kasancewar yadda basu kasa ba, har ma a gaban kayayyakin tsaron sararin samniyar Rasha ya sanya Bayraktar TB2 kasancewa akan gaba daga cikin jiragen tsaro marasa matuka a doron kasa.

 

Kwarewar jirage marasa matukan Turkiyya na IHA da SIHA ba su kasance masu cimma nasara a ayyukan leken asiri, sa ido kawai ba, har ma a ayyuka kamar murkushe tsarin tsaron sararin samaniya / makamai masu linzami ko kuma kawar da rukunin sulke na abokan gaba.

Wani lamarin da ya sanya kayayyakin tsaron kasar Turkiyya yin tasiri tsakanin kasashe kuma, shi ne rahusar da suke dashi. An dai san cewa wadanda Amurka ke yi sun fi tsada, bugu da kari fitar da irin wadanan kayan tsaro daga Amurka na bukatar tsanantawar amincewar wasu kaidoji dake kange wasu kasashe da dama daga samun damar sayensu daga Amurkan. Hakan ya baiwa jirage marasa matukan Turkiyya samun daman da kasashe suka fi gwamacewa su sayesu. Yarjejniyar sayen jirage marasa matukan Turkiyya da Poland ta yi, baya ga harkar tsaro ta na kuma tattare da lamurkan ikon yanki. Musanmman kasancewar Poland kamar Turkiyya a matsayar mamaban kungiyar NATO zai sanya kara dankon zumunci tsakanin Turkiyya da sauran mambobin kungiyar.

A gefe guda kuma, Poland kamar Yukiren wacce ke kallon Rasha a matsayar babbar kalubale a gabatanta, sayen wadannan makaman na karantar da wasu abubuwa daban. Ganin yadda bayan Yukiren ta sayi jiragen ne Poland kuma ta biyu ta a baya, na karanatar da wata hadakar  fuskantar tsarukan Rasha. Yadda kasashen dake makwabtaka da Rasha suka yi hadaka da Turkiyya na nufin Rasha ba ta da iko da damarmakin da ake tunanin ta mallaka yankin. Duk dai yadda Rasha za ta soki wadanan matakan na Turkiyya, hakika Ankara ba za ta yi ko in kula da korafinta ba.

 

Wanan sharhin Ferfefa Murat Yesiltas ne Daraktan Harkokin Tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA….


News Source:   ()