An sanar da cewa wani bam da aka ajiye kan babur a yankin Tal Abyad dake Arewacin Siriya ya tashi tare da kashe mutum biyu da kuma raunana wasu biyu a yankin.
Tun dai an gaggauta dauka wadanda suka samu raunin zuwa Turkiyya.
A yayinda jami'an tsaro suka kewaye yankin da lamarin ya faru, ana hasashen cewa kungiyar YPG/PKK ce ta kai harin.
An dai gudanar da farmakin tafkin zaman lafiya a ranar 13 ga watan Oktoban 2019 a yankin Tal Abyada dake arewacin Siriya.
Kungiyar ta'addar YPG/PKK na yawan kai hare-hare a yankunan Ayn Isazh da Tel Tamir da kuma yankunan Tal Abyad dake arewacin Siriya.