Taron COP29 na buƙatar dala tiriliyan 1 duk shekara don yaƙar illar dumamar yanayi

Taron COP29 na buƙatar dala tiriliyan 1 duk shekara don yaƙar illar dumamar yanayi

Taron na COP29 da batutuwa masu alaƙa da siyasa suka mamaye shi da ya kai ga janyewar wakilcin wasu ƙasashe irin Argentina, ya nemi amincewa ƙasashe musamman mawadata wajen ganin an tattara kuɗin da yawansu ya kai dala tiriliyan 1, da nufin magance matsalar ta sauyi ko kuma ɗumamar yanayi wadda tuni aka fara ganin illarta a muhallin ɗan adam.

Akwai fargabar kai ruwa rana gabanin iya cika wannan ƙudiri na fara samar da dala tiriliyan guda duk shekara kafin taron yanayi na COP30, da zai gudana a Brazil cikin shekara mai zuwa.

Buƙatar tattara wannan adadi mai matuƙar yawa na zuwa ne a wani yanayi da ake cike da taraddadi, kan ko zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump, zai ci gaba da mutunta yarjeniyoyin yanayi da ƙasar ta shiga ƙarƙashin mulkin Democrats, ta hanyar bayar da kason kuɗaɗen da aka dibarwa ƙasar a matsayin kuɗaɗen magance matsalar da sauyin yanayi ya haifar, wanda ke da nasaba da tiriri mai guba da masana’antun manyan ƙasashe ke fitarwa.

Illar wannan tiriri dai ya fi haifar da gagarumar matsala a ƙasashen Afrika da Asiya, waɗanda tuni suka fara fuskantar matsaloli masu alaƙa da ambaliyar ruwa da amon wutar dutse da zubar ruwa fiye da ƙima baya ga zaftarewa ƙasa dama girgizar ƙasa sai kuma zafi fiye da ƙima ko kuma sanyi fiye da ƙima, dama sauran birkicewar yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)