Taron na birnin Rome wanda za a shafe kwanaki 2 ana tattaunawa tsakanin shugabannin ƙasashen 7 mafiya ƙarfin tattalin arziƙi, kacokan zai mayar da hankali kan rikicin gabas ta tsakiya gabanin karkatawa zuwa rikicin Ukraine da Rasha, dai dai lokacin da Rasha ke ci gaba da luguden wuta a Kiev.
Ƙasashen na G7 za kuma su tattauna kan sammacin kamun Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kotun ICC ta bayar game da kisan ƙare dangin da ya ke yiwa falasɗinawa a Gaza, a wani yanayi da ministan wajen Italiya Antonio Tajani ke cewa fatan taron ya cimma daidaito don ganin an kawo karshen yaƙe-yaƙen da ke faruwa a gabas ta tsakiya musamman Lebanon.
Duk dai a taron na G7, Sakataren wajen Amurka Antony Blinken zai kuma yi tattaunawa da ta takwarorinsu na ƙasashen Birtaniya da Canada da Jamus da Faransa baya ga Japan da Italiya a biranen Fiuggi da Anagni, duk dai kan buƙatar Washington a yaƙin na gabas ta tsakiya.
Wani ɓangare na wannan taro zai ƙunshi wakilcin ƙasashen Saudiyya da Haɗaɗɗiyar daular larabawa da Masar da Jordan da kuma Qatar baya ga ƙungiyar ƙasashen Larabawa.
Taron dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake gab da ƙarƙare wata tattaunawa da ake fatan ta kai ga cimma matsaya kan tsagaita wuta a yakin da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI