Taron AI a Paris ya cimma matsaya kan matsalolin sassauta dokokin taƙaita amfani da ita

Taron AI a Paris ya cimma matsaya kan matsalolin sassauta dokokin taƙaita amfani da ita

A ƙalla ƙasashe 57 ne ciki har da Najeriya da Faransa, da ƙungiyar ƙasashen Afrika AU da takwararta ta Turai EU, da kuma ƙwararru sama da 200 suka rattaba hannu kan  ƙaddamar da gagarumin shirin, wanda manufofinsa suka ƙunshi, samar da tallafin bunƙasa fasahar AI, ƙarfafa ƙawance tsakanin kamfanoni masu zaman kansu da hukumomin gwamnati, da kuma haɗa gwiwa wajen daƙile duk wata barazana da ke tattare da ci gaban na kimsa wa na’ura basirar ɗan Adam.

Sanarwar ta ƙara da bayyana nazarin kimiyya, da tsara hanyoyin magance matsalolin da ka iya tasowa, da kuma kafa dokokin bai ɗaya na sa ido kan fasahar ta AI a matsayin manyan ginshiƙan da taron ƙasashen a Paris ya runguma, domin saita wa duniya alƙibilar da fasahar AI za ta fuskanta.

Da wannan ne dai wasu ƙwararrun ke ganin an kawo ƙarshen fargabar da hukumomin ƙasa da ƙasa ke yi a kan haɗurran da ke tattare da AI ta fuskar tsaro da sauran fannonin rayuwar ɗan Adam, matsalolin da ƙwararru suka tafka muhawara a kai, yayin tarukan da suka yi a Birtaniya da Korea ta Kudu a 2023 da kuma 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)