Ƴan ciranin fiye da dubu 2 ne yanzu haka suke wani tattaki cikin ayari daga kudancin Mexico cike da fatan isa Amurka kafin rantsar da Donald Trump a ranar 20 ga watan Janairun 2025, ƴan gudun hijirar da bayanai ke cewa sun fito daga mabanbantan ƙasashen latin Amurka.
Tattakin ƴan ciranin na zuwa a wani yanayi da ake cike da fargabar makomar ƴan ciranin da ke rayuwa a cikin Amurka lura da alwashin da shugaban mai jiran gado ya ci na ganin ya tiso ƙeyar dukkanin baƙin da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.
Rahotanni sun ce ayarin ƴan ciranin sun faro tattaki daga ranar 1 ga watan nan bayan tattaruwa a garin Tapachula na kudancin Mexico gabanin faro tattakin, balaguron da ke gudana bisa rakiyar tarin ƴan fafutukar kare haƙƙin ƴan cirani tare da jami’an agaji lura da haɗarin da ke tattare da tafiyar.
A cewar bayanai tun farko akwai dubban ƴan ciranin ƙasashe kudanci da tsakiyar Amurka waɗanda ke rayuwa a sassan Mexico cike da fatan samun damar tsallakawa Amurka wani lokaci a nan gaba, sai dai nasarar Trump a zaɓen Amurka ya wargaza tunaninsu tare da sanyasu a fargabar yiwuwar rasa damar shiga ƙasar lura da alƙawurran shugaban na daƙile kwararar baƙi cikin ƙasar, dalilin da ya sanya su shiga wannan balaguro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI