Tarihin jagoran Hamas da aka kashe a Tehran

Tarihin jagoran Hamas da aka kashe a Tehran

Shin wane ne Ismail Haniyeh?

Ya kasance shugaban siyasar ƙungiyar Hamas kuma shi ne tsohon firaministan Falasɗinu, sannan yana cikin mambobi na farko da aka kafa ƙungiyar Hamas da su.

An haifi Haniyeh a shekarar 1963 a sansanin ƴan gudun hijira ta Al-Shati da ke Zirin Gaza bayan iyayensa sun yi ƙaura daga Ashkelon a lokacin fafutukar ƙafa kasar Isra'ila.

A lokacin samartakarsa, Haniyeh ya kasance mamba a Ƙungiyar Ƴan uwa Musulmi a Jami'ar Gaza, sannan ya shiga cikin ƙungiyar Hamas ne a shekarar 1987, lokacin da aka ƙafa ƙungiyar bayan ɓarkewar zanga-zangar Intifada ta farko a Falasɗinu don nuna adawa da mamayar Isra'ila.

Ƴan Hamas na gabatar da zanga-zangar nuna adawa da kisan Haniyeh Ƴan Hamas na gabatar da zanga-zangar nuna adawa da kisan Haniyeh © Mohammed Zaatari / AP

Haniyeh ya kasance hadimi ga shugaba kuma wanda ya assasa Hamas, Sheikh Ahmed Yassin, inda sannu a hankali ya yi ta samun ƙarin matsayi har sai da aka wayi gari shi ma ya zama jagoran siyasar wannan ƙungiyar a shekarar 2017.

 

Haniyeh da mai gidansa sun taɓa tsallake rijiya da baya

Haniyeh da mai gidansa Yassin sun taɓa tsallake rijiya da baya a wani yunƙurin kashe su da aka yi a shekarar 2003, inda a wancan lokacin suka fito cikin koshin lafiya daga cikin gidan da Isra'ila ta yi wa luguden bama-bamai. Kodayake Yassin ya rasu bayan shekara guda da wannan farmakin.

Haniyeh ya yi ƙaura don ratsin kansa zuwa Qatar tun shekarar 2019, yayin da duk wata barazanar da ake yi masa ta gaza hana shi tafiye-tafiyensa. 

Ya ziyarci Turkiya da Iran a daidai lokacin da ake gwabza yaƙi tsakanin Hamas da Isra'ila. Ya kuma kasance cikin masu ruwa da tsaki a tattaunawar tsagaita musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu da aka gudanar a birnin Doha.

Minisatan Harkokin Wajen Iran  Hossein Amir Abdollahian tare da Ismail Haniyeh a birnin Doha na Qatar a ranar 14ga watan Oktoban 2023 Minisatan Harkokin Wajen Iran Hossein Amir Abdollahian tare da Ismail Haniyeh a birnin Doha na Qatar a ranar 14ga watan Oktoban 2023 via REUTERS - WANA NEWS AGENCY

Yadda aka kashe ƴaƴan Haniyeh a wani harin Isra'ila

Marigayin ya rasa iyalansa da makusantansa, inda a cikin watan Afrilu Isra'ila ta ƙaddamar da wani farmaki da ya yi sanadiyar mutuwar ƴaƴansa uku a Gaza.

Kazalika Hamas ta ce, an kuma kashe jikokin Haniyeh har guda huɗu da kuma ƴar uwarsa a wasu mabanbantan hare-hare a cikin watan jiya.

Haniyeh ya kware wajen gabatar da maƙala

Haniyeh ya kasance mai riƙo da addini, sannan ya karanci adabin Larabci a jami'a. Kazalika ya yi fice wajen gabatar da dogayen makala tare da amfani da kyawawan kalamai don kayatar da mabiyansa a lokacin da yake rike da kujerar firaminista.

Haniyeh ya zama firaminista ne a gwamnatin Falasɗinu bayan Hamas ta lashe zaɓen ƴan majalisa a shekarar 2006. Ya jagoranci rikici mafi girma da Falasɗinu ta tsinci kanta a ciki a tarihinta, rikicin da har yanzu ake fama da shi.

Ismail Haniyeh tare da muƙarrabansa Ismail Haniyeh tare da muƙarrabansa © Mohammed Salem / Reuters

Hamas ta ce, an kashe Haniyeh a gidansa da ke Tehran sakamakon wani harin sama da aka ƙaddamar masa bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban Iran. Amma kawo yanzu, Isra'ila ba ta ce uffam ba game da zargin da ake yi mata na kisansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)