Majalisar Tarayyar Turai za ta kaddamar da dokar sai in mutum nada takardan shaidan allurar riga-kafin Korona ne zai iya shiga nahiyar.
Wani mamban majalisar Ylva Johansson, ya amsa tambayoyin manema labarai game da satifiket din allurar riga-kafin Koronan.
Johansson, ya bayyana cewa majalisar za ta amince da dokar sai in masu zuwa yawun bude ido na da satifiket din allurar riga-kafin Korona ko kuma passeport din Korona ne zasu iya shiga nahiyar.
Ana sa ran majalisar za ta tabbatar da wacannan dokar a zaman da za ta yi a ranar 17 ga watan Maris wanda kuma za ta fitar da cikekken bayani a ranar.
Kawo yanzu dai Tarayyar Turai ta amince da alluran riga-kafin kanfunan BioNTech-Pfizer, Moderna da AstraZeneca.
Haka kuma tarayyar ta karbi allurran riga kafin Koorna na kanfanin Johnson&Johnson wanda za ta amince dashi da kuma bayar da umarnin fara amfani dashi a watan Afirilu.