Tarayyar Turai za ta dauki mataki akan sauyin yanayi

Tarayyar Turai za ta dauki mataki akan sauyin yanayi

Kasashe Tarayyar Turai sun yanke shawarar rage hayakin gas da suke fitarwa da kashi 55 cikin 100 nan da shekarar 2030 don yaki da canjin yanayi.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya fitar da wata sanarwa ta shafin sada zumunta yayin taron Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai da aka gudanar a Brussels, babban birnin Belgium.

Michel ya bayyana cewa shugabanin sun mayar da hankali akan daukar matakan rage sauyin yanayi inda suka yanke hukuncin rage yawan hayakin gas da kanfuna ke fitarwa.

Michel, ya tabbatar da cewa nan da shekarar 2030 za a rage kaso 55 cikin darin hayakin gas din da ake fitarwa a halin yanzu.

 


News Source:   ()