Tarayyar Turai ta yi kira ga Azerbaijan da Armeniya da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta

Tarayyar Turai ta yi kira ga Azerbaijan da Armeniya da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta

Tarayyar Turai ta yi kira ga kasashen Azerbaijan da Armeniya da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar Nagorno-Karabakh da suka ayyanar a tsakaninsu.

Shugaban Kwamitin Tarayyar Turai Charles Michel, ya yada a shafukansa na sadar da zumunta da cewa yarjejeniyar tsagaita wutar da kasashen Azerbaijan da Armeniya suka yi a tsakaninsu abu ne mai muhinmanci kwarai da gaske.

"Muna kira ga dukkanin bangarorin da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma, su kuma gujewa dukkan matakin da zai kara tada kayan baya da jefa farar hula cikin halin kaka-nikayi."

Michel, ya kara da cewa ya kamata bangarorin biyu su fara zaman sulhu nan take.

Kasashen Armeniya da Azerbaijan sun ayyanar da yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakaninsu a ranar 10 ga watan Oktoba da misalin karfe 12:00 da zummar bayar da damar kaiwa farar hula dauki da kuma yin musayar fursunoni da matattu a tsakaninsu.

Amma bayan yarjejeniyar ko awanni 24 ba'a yi ba, Armeniya ta kai harin roka a garin Gence lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar farar hula 11 da raunanan 35.

 


News Source:   ()