Tarayyar Turai ta dakatar da rarraba takunkuman rufe fuska na China

Tarayyar Turai ta dakatar da rarraba takunkuman rufe fuska na China

Hukumar Tarayyar Turai ta dakatar da rarraba takunkuman rufe fuska da ta saya daga China zuwa kasashe mambobinta bayan korafe-korafen rashin ingancinsu.

Hukumar Turai ta yi odan takunkumai har kwara miliyan 10 daga China domin taimakawa cibiyoyin lafiyar kasashen nahiyar.

Ta kashe zunzurutun kudade har dala miliyan 2.9 domin daukar matakan gaggawa yakar coronavirus.

Da farko dai an shigo da takunkumai har kwara miliyan 1.5 wadanada aka rarraba a mambobin nahiyar 17 da kuma Birtaniya.

Amma abubuwan kariyar basu kai ingancin tsarin nahiyar Turai ba sabili da hak aba za’a iya amfani dasu ga masu jinyar masu fama da Covid-19 ba kamar yadda ministan lafiyar Poland Minister Lukasz Szumowski ya sanar da tarayyar.


News Source:   www.trt.net.tr