Tarayyar Turai na shirin baiwa Boeing 737 Max izinin tashi a kasashenta

Tarayyar Turai na shirin baiwa Boeing 737 Max izinin tashi a kasashenta

Tarayyar Turai na shirin bayar da izini ga jirgin sama samfurin Boeing 737 Max da aka hana amfani da shi bayan hatsarin da ya yi.

Daraktan Hukumar Kula da Lafiyar Jiragen Sama ta Turai Patric Ky, ya yi bayanai game da jirgin saman Boeing Max 737 da ake samarwa a Amurka wanda aka amfani da shi bayan hadurran da suka afku a shekarun 2018 da 2019.

Ky ya ce, a mako mai zuwa ake shirin bayar da izini ga Boeing 737 Max don fara tashi a kasashen Turai.

Daraktan ya kara da cewa, da fari an fara kokarin gano yadda hatsarin ya afku, kuma an kara karfin tsaron jiragen saman tare da yin sauye-sauye masu kyau.

A shekarar da ta gabata Amurka da Barazil suka bayar da izinin ci gaba da tashi da saukar Boeing 737 Max.


News Source:   ()