An gudanar da Babban Taro na "Babban Kwamitin Kungiyar Tarayyar Kasashen Musulmi ta (OIC), da gabatarwar Turkiyya a matakin Ministocin Harkokin Waje ta hanyar bidiyo konferans.
Bayan taron, Sakatare Janar na OIC, Yusuf bin Ahmed al-Useymin ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su "dauki nauyin da ke kansu na dabi'a, jin kai da kuma doka" don dakatar da hare-haren da sojojin Isra'ila ke kaiwa kan Falasdinawa tun daga ranar 10 ga watan Mayu.
Useymin ya kara da cewa:
"Hare-hare, gami da kwace dukiyar Falasdinawa, da kuma mamaye masu yankunasu na halal, ba sa aiwatar da shirin zaman lafiya. Akasin haka, yana kawo cikas ga kokarin da ake yi na gaskiya don cimma daidaito, cikakke kuma mai dorewa."
Ministan Harkokin Wajen Jordan Eymen al-Safedi, wanda ya halarci taron, ya bayyana cewa, tilasta wa mazauna yankin Sheikh Jerrah Quarter na Gabashin Kudus da Isra'ila ta mamaye ficewa daga yankin, laifi ne na yaki da kasashen duniya ba su yarda da shi ba.
A nasa jawabin, Ministan Harkokin Wajen Pakistan Shah Mahmud Qurayshi, shi ma ya yi kira ga kasashen duniya da su sa baki tare da daukar matakin da ya dace don dakatar da musgunawar da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa.
A jawabinsa a wajen taron, Ministan Harkokin Wajen Falasdinu Riyad al-Maliki ya bayyana cewa, Isra'ila ta aikata laifuka tare da yin amfani da tashin hankali a kan jama'a a Zirin na Gaza da ke karkashin mamayarta.
Ya kuma tabbatar da cewa,
"Ci gaba da hare-haren bama-bamai a Gaza ya haifar da rasa matsugunan Falasdinawa sama da 10,000 tare da lalata daruruwan gidaje a duk yankin."