Manasa kiwon lafiya sun sanar da cewa babu wata takamammiyar amsa akan tambayar iya lokacin da mutun zai kasance tare da mai cutar Korona kafin ya kamu da cutar.
Cibiyar Kula da Yaduwar Cututtuka ta kasar Amurka watau CDC, a ‘yan kwanakin baya ta sauya bayanan da ta yi akan yadda ake tabbatar da mutum ya kusance mai dauke da Korona, ta kuma bayar da shawarar cewa duk wanda ya kasance kusa da mai cutar Korona ya zama wajibi ya kebe kansa daga bisani kuma ayi masa gwajin cutar.
Ferfesa Henry Raymond, a jami’ar Rutgers ya bayyana cewa kusantar mai Covid-19 ba shi tabbacin cewa mutum zai iya kamuwa da cutar ba, ya ta’alaka akan yanayin gurin da mutum ya kusanci mai cutar idan akwai wadatacciyar iska ko babu da kuma ko suna sanye da takunkumi ko a’a da kuma ko akwai cudanya a tsakaninsu ko babu.
A kwanakin baya dai, kusantar mai Korona ana bayyana shi ne a matsayin wanda ya kasance tare da mai cutar Covid-19 na mintuna 15 da nisan da bai wuce kafa shidda ba. A halin yanzu kuwa, wanda ya kusanci mai Korona ana bayyana shi a matsayin wanda ya kasance tare da mai cutar da tazarar da bai wuce kafa shidda ba na akallan mintuna 15 a cikin awanni 24.