Tambayar Mako: Ko ana kamuwa da kwayar cutar Korona sau biyu

Tambayar Mako: Ko ana kamuwa da kwayar cutar Korona sau biyu

Malaman kiwon lafiya sun bayyana cewa akwai alamun cewa za’a iya sake kamuwa da kwayar cutar Korona karo na biyu bayan warkewa daga cutar a karo na farko.

Masu binciken kwakwan dake birnin New York a Amurka sun gano cewa sake kamuwa da cutar Korona a karo na biyu ka iya kasancewa bayan watanni uku da warkewa daga kamuwa da cutar karo na farko. Bugu da kari kungiyar ta gano mutum 20,000 wadanda suka kasance cikin tsanaki daga cutar a asibitin Mount Sinai.

A hakikanin gaskiya dai sake kamuwa da cutar Covid-19 karo na biyu abu ne wanda ba’a cika samu ba. A wani bincike da aka gudanar a Hong Kong ya nuna cewa wa samu wani mutun da ya taba kamuwa da Korona bayan ya warke da wata daya kuma aka sake samun shi dauke da ita. An tabbatar da sake kamuwa da cutar da yayi a wani gwaji da aka yi a wani filin tashi da saukar jiragen sama inda masana suka bayyana cewa cutar da aka sake samu a jikinsa nada dan babbanci da ainihin cutar ta farko.

An tabbatar da cewa garkuwar jikin mutumin ta yi aiki yadda ya kamata sabili da cututtuka ‘yan kadan ne ke barin mutun garkuwar jikin mutum ta yi aiki baki daya.

Jaridar Daily Sabah ta Rawaito cewa, a Nevada dake Amurka an dan samu irin hakan ga wani mutum mai shekaru 25 a ranar 18 ga watan Afirilu an yi masa gwajin Korona inda aka sameshi dauke da ita. Bayan kwanaki 35 an sake garzayawa dashi zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa ya sake kamuwa da Korona.

 


News Source:   ()