Tallafi daga Turkiyya ga yankin da aka gudanar da Farmakin Tafkin Zaman Lafiya a Siriya

Tallafi daga Turkiyya ga yankin da aka gudanar da Farmakin Tafkin Zaman Lafiya a Siriya

Ana koyar da ilimin addini a yankin Tal Abyad na Siriya, wanda aka tsarkake daga kungiyar ta'adda ta a ware YPG/PKK da Farmakin Tafkin Zaman Lafiya (daga Oktoba zuwa Nuwamban 2019) tare da goyon bayan Turkiyya.

Danagne da sanarwar da Gwamnan Sanliurfa ya fitar, ana ci gaba da koyar da ilimi da dabi’u a Tal Abyad karkashin kulawar Cibiyar Tallafawa da Kula da Siriya ta Sanliurfa ta Gwamnati (SUDKOM).

A cikin wannan mahallin, a Tal Abyad inda rayuwar yau da kullum ke komawa yadda take a da ana bayar da darussan Alƙur'ani bisa buƙatun mutane.

A cikin aiyukan koyar da ilimin addini da aka gudanar karkashin hadin gwiwar Kawancen Ayyubiye a Sanliurfa, akwai mutane 45 a Masallacin Abu Talip a tsakiyar Tal Abyad, 50 a Masallacin Ravza, 14 a Masallacin Musab Bin Umeyr, 20 a Masallacin Darul Etyam, 25 a cikin ƙauyukan Cenubiye da Sarkiye. Kimanin 154 a cikin wadanda aka horar sun kammala haddar Alkur’ani kuma an ba su takardar shaidar nasarar a wani buki.

A gefe guda kuma, yara dubu shida a Tal Abyad sun sami tallafi na zamantakewa na motoci masu sinima na yara a makarantu 35.


News Source:   ()