Taliban ta yi kira ga ma'aikatan kiwon lafiya mata da su koma bakin aiki

Taliban ta yi kira ga ma'aikatan kiwon lafiya mata da su koma bakin aiki

Taliban ta bukaci ma’aikatan lafiya mata a Afghanistan da su koma bakin aikinsu.

Zabihullah Mujahid, daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar ta Taliban, ya sanar da cewa an kira ma’aikatan kiwon lafiya mata na ma’aikatar lafiya da su ci gaba da ayyukansu a wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter.

Mujahid, a cikin sakon nasa, ya jaddada cewa sabuwar gwamnatin ba ta da matsala da ma'aikatan kiwon lafiya mata na ci gaba da aikinsu,

"Ma'aikatar lafiya ta sanar da dukkan ma'aikatan mata a larduna da babban birnin kasar da su ci gaba da aikinsu." 

Mai magana da yawun kungiyar Mujahid ya shawarci mata a Afganistan da kar su fita daga gida har sai an dawo da tsaro a kasar, amma ya ce wannan "hanya ce ta wucin gadi".

Dangane da damuwar cewa Taliban za ta tauye 'yancin mata a Afganistan, Mujahid ya sanar da cewa sabuwar gwamnatin na ci gaba da kokarin tabbatar da dawo da ma'aikatan gwamnati mata aikin su.


News Source:   ()