Taliban ta kwace wasu gundumomi a Afghanistan

Taliban ta kwace wasu gundumomi a Afghanistan

An bayyana cewa wasu gundumomi 2 a lardin Faryab dake kasar Afghanistan sun koma hannun Taliban.

Dan majalisar Faryab, Babur Jamal ya fada a cikin wata sanarwa ga manema labarai cewa mayakan sun kai wani hari da makami a gundumomin Karamkol, Kurgan da Andhoy na Faryab.

Da yake bayyna cewa gundumomin Karamkol da Kurgan suna karkashin ikon Taliban sakamakon harin, Cemal ya bayyana cewa ana ci gaba da arangama a kusa da gundumar Andhoy.

Cemal ya yi ikirarin cewa hukumomin tsaro ba su yi wani kwakkwaran bincike kan wannan batun ba.

A cikin wata sanarwa da kungiyar Taliban ta fitar, ta yi ikirarin cewa gundumomin Karamkol, Kurgan da Andhoy suna hannunta baki daya sakamakon harin da suka kai.

Gundumar Gurzivan na lardin Faryab ya koma karkashin ikon Taliban.

Ma'aikatar Tsaro ta Afghanistan ta sanar da cewa, an kashe 'yan ta'adda 129 a yayin fatattakar 'yan kungiyar Taliban a larduna 9 na kasar.

A cikin sanarwar an kara da cewa 'yan bindiga 35 sun ji rauni a yayin samamen, an kuma jaddada cewa an lalata bama-bamai 31 da aka shirya kai hari dasu.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa sakamakon faramakan da aka kai an kwato gundumomi da dama daga hannun Taliban.

Fada ya ci gaba tsakanin jami’an tsaro da ‘yan Taliban a mafi yawan kasashen Afghanistan, kuma ana ci gaba da gwabza fada a kusan gundumomi 200 daga cikin 407.


News Source:   ()