An sanar da cewa harin bam da aka kai a garin Hash dake jihar Badahshan a kasar Afghanistan ya hallaka mutum 11.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Badahshan Sanaullah Ruhani, ya shaidawa manema labarai da cewa wani bam da aka ajiye a gafen hanya a garin Hash dake yankin Durhan ya tashi yayinda 'yan sanda ke wucewa.
Tashin bam din ya yi sanadiyar rayukan 'yan sanda 11, an kuma dora alhakin harin akan kungiyar Taliban.
Kawo yanzu dai Taliban bata ce komai ba akan al'amarin.