A kasar Afghanistan kungiyar Taliban ta ta kai hari a wani ofishin 'yan sanda lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan 'yan sanda 8.
Mai magana da yawun 'yan sandan kasar Adilsha Adil ya bayyana cewa a yankin Belh dake arewacin kasar a kauyen Shahrek Turkmeniye dake kusa da garin Nahri Shahi an kai hari a ofishin 'yan sanda.
A harin an kashe 'yan sanda 8 da kuma raunana wasu 4 haka kuma an magance maharan 5 da raunana 7 daga cikinsu.
Kungiyar Taliban ta yi ikirarin cewa ta kashe sojoji 12 a harin.