Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Afganistan ta bayyana cewar fararen hula 20 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren da 'yan ta'addar Taliban suka kai a lokacin bukukuwan Sallar Layya.
Kakakin ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Afganistan Tarik Aryen ya shaida cewar a hare-haren da Taliban ta kai wasu fararen hular 40 sun jikkata.
Ya shaida cewar 'yan ta'addar sun kari da bam da bindigu a lokacin bukukuwan Sallah wanda ya ke tabbatar da Taliban ba ta cika alkawarin da aka kulla da ita na tsagaita wuta.
Aryen ya kara da cewar dakarun gwamnati sun yi iki da yarjejeniyar sabanin Taliban.
Sanarwar da Taliban ta ce mayakanta ba su karya yarjejeniyar ba.