Taliban ta hallaka jami'an tsaro 20 a Afganistan

An sanar da cewa a harin da kungiyar Taliban ta kai a wani ofishin 'yan sanda a wani gari dake kasar Afganistan 'yan sanda 20 sun rasa rayukansu.

Lamarin ya afku ne a garin Hashrud dake yammacin jihar Nimruz inda yan bindigan suka kai harin bindiga a wani ofishin 'yan sandan Dehmezeng kamar yadda shugaban yankin Celil Vatandost ya bayyana.

Vatandost dake bayyana cewa jami'an tsaro 20 sun rasa rayukansu ya kara da cewa an yi nasarar kame mayakan da suka kai harin har su shida.

Kawo yanzu dai Taliban bata ce kmoai ba game da lamarin.

A dayan barayin kuma ma'aikatar tsaron kasar Afganistan ta sanr da cewa a cikin awnni 24 mayakan sun kai hari a garuruwa 24 a fadin kasar.

 


News Source:   ()