Taliban: Muna son kulla kyakkyawar alaka da Turkiyya

Taliban: Muna son kulla kyakkyawar alaka da Turkiyya

Kakakin Ofishin Siyasar Taliban a Katar Muhammad Naim Vardak ya shaida cewa, suna da sha'war kulla kyakkawar alaka mai inganci tare da Turkiyya.

Vardak da yake bayani bayan da Taliban ta kwace iko da Kabul Babban Birnin Afganistan ya ce,

"Turkiyya kasa ce mai muhimmanci, Al'umar Turkiyya 'yan uwa ne Musulmai kuma abokai. Muna da alaka ta al'adu da zamantakewa da Turkiyya."

Vardak ya kara da cewa, a nan gaba suna bukatar habaka dangantakarsu da Turkiyya, kuma a yanzu suna tattaunawa.

Da aka tambayi Vardak ko Taliban na bukatar taimakon Turkiyya sai ya kada baki ya ce,

"Babu kokonto game da haka. Muna son taimako. Al'umarmu ta shekara 40 tana yaki a saboda haka tana bukatar taimako. Muna so dukkan duniya musamman ma Turkiyya da su taimakawa kasarmu."

Ya ci gaba da cewa, Turkiyya na da matukar muhimmanci wajen sake gina Afganistan, kuma za ta iya taka muhimmiyar rawa mai kyau wadda Afganistan ke bukata.

Game da yanayin alakar kasashen biyu Vardak ya ce,

"Akwai tushe guda biyu a alakarmu. Na farko shi ne dokokin Addinin Musulunci, na biyun su kuma shi ne amfanar kasar da jama'arta. Sakamakon wadannan abubuwa guda biyu, muna son mu kulla kyakkayawar alaka da Turkiyya. Bamu da wata matsala da Turkiyya."


News Source:   ()