Sabanin takunkuman da Amurka ta kara kakkabawa Iran kasar ta bayyana cewa zata cigaba da ayyyukan kera makaman nukiliya.
Kafar talabijin din kasar ta yada cewa matakin Amurka na kakkabawa wasu masanan kimiyya da fasahar makaman nukiliyar Iran takunkumi alamace ta cigaba da halin rashin jituwa tsakanin kasashen biyu kuma lamari ne da zai sanya kasar cigaba da ayyukan kera makaman nukiliya.
Bayanin ya yi ikirarin cewa takunkuma sun sabawa dokar kasa da kasa.
A ranar Laraba ne dai ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kakkaba takunkumai akan Iraniyawa biyu masana kimmiyar nukiliya da suka ha da Majid Agha da Amjad Sazgar wandanda ke da ruwa da tsaki a yunkurin habbaka harkokin yuraniyom.