A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X Harris ta ce tana farin cikin sanar da Tim Walz a matsayin mataimakinta a takarar shugabancin ƙasar.
Takaitaccen tarihin Tim Walz
An haifi Tim Walz a ranar 6 ga watan Afirlu na 1964 a wani yanki mai suna West Point a jihar Nebaraska, yanzu haka yana da shekaru 60 a duniya.
Ya halarci kwalejin Chadron inda ya yi digirin na farko a fannin ilmin zamantakewa a shekarar 1989.
Ya share shekara 24 yana aikin soja bayan da ya shiga tun yana ɗan shekara 17 a duniya.
Ya auri matarsa mai suna Gwen a shekarar 1994 inda suka koma kudancin jihar Minnesota suka fara aikin koyarwa da horar da ƴan wasa a makarantar Mankato.
Ya yi aikin koyarwa a ƙasar China kafin ya koma gida Amurka ya ɗora aikin koyarwa a babbar makarantar Alliance.
Cibiyar Kasuwanci a jihar Nebaraska ta taɓa ayyana shi a matsayin matashi mafi hazaka dake bada gudunmawa a fannin ilmi.
Tim Walz mamba ne a jam’iyyar Democract ya zama ɗan majalisa mai wakiltar yankin Minnesota daga shekarar 2007 zuwa 2018.
An zabi Tim Walz gwamnan jihar Minnesota a 2018 tare da sake zama gwamna a karo na 2 a shekarar 2022.
Tim Walz na cikin masu goyan bayan Isra’ila tun da ya shiga sha’anin siyasa, kuma ya caccaki ɗauko JD Vance da Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban ƙasar Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI