Tajikistan ta tilasta yin allurar riga-kafin Korona a fadin kasar

Tajikistan ta tilasta yin allurar riga-kafin Korona a fadin kasar

A Tajikistan, yin allurar riga-kafin sabon nau'in coronavirus (Kovid-19) ya zama tilas ga ‘yan sama da shekaru sama da 18.

Tare da shawarar da Hukumar Tajikistan ta Anti-Coronavirus ta yanke, yin allurar rigakafi a cikin kasar ya zama tilas ga yan shekaru sama da 18.

An kuma fara aiwatar da aikin kiyaye wadanda suka shigo kasar daga kasashen waje a kebe su na tsawon kwanaki 10.

A yayinda aka samar da doz na dubu 192 na allurar riga-kafin Vaxzevria da aka samar da hadin gwiwar allurar AstraZeneca ta jami'ar Oxford,  da kuma wanda kanfanin Sinovac na kasar China ya kirkira har dubu 300, ana sa ran samar da na kasar Rasha Sputnik V har dubu 100 nan da 'yan kwanaki.

A kasar da aka fara aikin rigakafin a ranar 22 ga Maris, mutane dubu 280 ne aka yi wa rigakafin kawo yanzu.

Ya zuwa yanzu, mutane 92 sun mutu a cikin annobar Kovid-19 a ƙasar.


News Source:   ()