Taiwan zata saye jiragen yaki kirar F-16 daga Amurka

Taiwan zata saye jiragen yaki kirar F-16 daga Amurka

An sanar da cewa kasar Taiwan ta yi yarjejeniya akan jiragen yaki kirar F-16 da katabaren kanfanin tsaron Amurka mai suna Lockheed Martin.

Kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta Pentagon ta sanar a rubuce, Lockheed Martin da Taiwan sun rataba hannu akan yarjejeniyar siyar jiragen yaki 90 kirar F-16.

Dangane ga yarjejeniyar za'a kammala shirin sayen jiragen yakin ne zuwa shekarar 2026.

Wacanan yarjejeniyar ta dauki hankalin al'umma musanman yadda ta tabbata a daidai lokacin da Amurka da China ke yiwa juna kallon hadarin kaji.

 


News Source:   ()