Ministan harkokin wajen Isra’ilan Katz yayin zantawarsa da babban jami’in diflomasiyyar Faransa da ke ziyara a ƙasar ya ce suna da ƙwarin gwiwar cewa ƙawayen Isra’ila baza su zuba ido ba muddin Iran ta farmake su.
Iran da ƙawayenta sun sha alwashin ɗaukar fansa kan kisan jagoran Hamas Isma’il Haneyah a Tehran cikin watan jiya, kisan da aka ɗora alhakinsa kan Isra’ila, ko da ya ke har yanzu ƙasar ba ta ɗauki alhakin hakan ba.
Ko a Alhamis ɗin makon nan da aka faro tattaunawar tsagaita wuta a yaƙin na Isra’ila a Gaza wadda Qatar ke ɗaukar nauyi bisa wakilcin manyan ƙasashe ciki har da Amurka, Iran ta nanata cewa cimma jituwar tsagaita wuta a yaƙin na Gaza ne kaɗai zai kange ta daga kai farmaki Isra’ila.
Sai dai zantawar tsakanin Katz da Stephane Sejourne da kuma David Lammy na Birtaniya, ministan wajen na Isra’ila ya ce suna da fatan ƙawayenta su taya ba kaɗai kare kansu ba, har da kai farmaki cikin Iran da kuma kadarorinta na ciki da wajen kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI