Mulibazisi Ngwenya, mai shekaru 79, ya zauna a farfajiyar shagonsa da aka rufe a Maranda, wani karamin gari a Zimbabwe, yana tunawa da kwanakin da ake hada-hada a kantinsa na kayan miya.
Yanzu yana da matsalar rashin lafiya da kuɗi, kuma yana neman masu hayar shagon sa a Maranda, karamin cibiyar kasuwanci a gefen arewacin gundumar Mwenezi a lardin Masvingo, wanda ke kewaye da duwatsu masu tsakuwa.
Masu haya sun karbi shagonsa amma sai suka kaurace a cikin 'yan shekarun da suka gabata saboda karancin tattalin arziki. Ngwenya yanzu ya rasa begen sake yin hayan shagonsa, duk da cewa yana bukatar kudi don karin abin da yake samu a matsayinsa na wanda shekaru suka yi wa yawa.