An haifi Yahya Sinwar ranar 29 ga watan Oktoban 1962, a sansanin ƴan gudun hijira na Khan Younus da ke zirin Gaza guda cikin sansanonin farko-farko da aka samarwa Falasɗinawan da Isra’ila ta tilastawa barin matsugunansu bayan yaƙin da ta gwabza da ƙasashen Larabawa a shekarar 1948.
Tun daga shekarun Yarinta Sinwar ya tashi da gwagwarmayar fatan ƙwatarwa Falasɗinawa ƴanci daga mamayar Isra’ila, inda ya shiga sahun waɗanda suka assasa ƙungiyar Hamas a shekarar 1987 tare da kafa sashen ƙungiyar masu riƙe da makamai, gabanin kameshi a shekarar 1988 bayan kisan wasu Sojin Isra’ila 2 inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai har ruɓanye 4, ko da ya ke yana daga cikin waɗanda aka saki yayin yarjejeniyar Shalit da ta kai ga musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila a shekarar 2011.
Jagoran kungiyar Hamas Yahya Sinwar. REUTERS/Mohammed Salem/File PhotoSinwar ya yi karatu a matakin jami’a a cikin yankin na Falasɗinu inda ya karanta harshen Larabci da ilimin addinin Islama, kasancewarsa jigo a Hamas, kai tsaye ya shiga sahun shugabannin ƙungiyar inda ya ke tsara kai hare-hare kan Isra’ila, hasalima shi ya tsara harin ranar 7 ga watan Oktoba, kuma tsaurin aƙidarsa ya haddasa saɓanin fahimta tsakanin shugabannin ƙungiyar waɗanda ke ganin akwai sauran lokaci gabanin fara yaƙi, yayinda Sinwar a nasa ra’ayin ke ganin wannan shi ne lokaci.
Masharhanta na kallon Sinwar a matsayin mai tsattsauran ra’ayi batun da wasu ke ganin na da nasaba da azabtarwar da ya fuskanta a hannun Yahudawa, inda jim kaɗan bayan fitowarsa daga yari ya bayyana cewa fatansa shi ne farmakar Isra’ila tare da karya wayar da ta raba yankin da ƙasar da ke matsayin mallakin Gaza a Taswira.
Gabanin kai harin ranar 7 ga wata da Sinwar ya tsara, wani hotonsa ya yi yawo a lokacin da ya ke kallon agogon hannunsa da rubutun cewa bashi da lokacin ɓatawa wajen samar da ƴanci ga ɗimbin Falasɗinawan da ke tafe a ƙarni na gaba.
Yahya Sinwar. © Mohammed Salem / ReutersA shekarar 2012 ne Sinwar ya fara riƙe muƙami ƙarƙashin Hamas bayan Isra’ila ta kashe Ahmed Jabaari jagoran Qassam Brigates wannan ya bashi damar samar da rundunonin tsaro na musamman tare da atisayen hare-haren kan Isra'ila irinsu March of Return daga 2018 zuwa 2019 sai Operation Sword of Jerusalem a shekarar 2021 kana Operation Al-Aqsa Flood daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023 zuwa yanzu, wanda dukkaninsu aka gwabza yaƙi tsakanin ƙungiyar da Isra’ila.
Duk da cewa amfani da ramukan ƙarƙashin ƙasa ba sabon salon yaƙi ne da Hamas ke amfani da shi ba, sai dai ƙarƙashin jagorancin Sinwar ya faɗaɗa salon ta yadda suka samar da yanki guda na musamman a ƙarƙashin ƙasa ciki har da gini mai hawa 15 a ƙasan ƙasa.
Ko da ya ke Yahya Sinwar ya yi galaba wajen kai hare-hare kan Isra’ila ko kuma kisan tarin Yahudawa, amma jagorancinsa ya haddasawa yankin na Gaza gagarumin koma baya musamman ganin yadda yankin ke fuskantar ƙawanyar tun shekarar 2007.
A wata zantawarsa da ɗan jaridar Italiya Francesca Borri, Yahya Sinwar ya ce ko kaɗan baya kallon kansa a matsayin wanda ya fita daga gidan yari face wanda aka sauyawa matsuguni daga wani yari zuwa wani, domin a cewarsa rayuwa a yankin Gaza ya fi yari tsauri.
Har kullum fatan Sinwar shi ne samar da ƴanci da kuma ingantacciyar rayuwa ga Falasɗinawan da ke tasowa kamar yadda ya ke bayyanawa a mabanbantan hira da manema labarai.
Rahotanni sun ce Sinwar ya gamu da ajalinsa ne lokacin da ya ke sintiri a gajeruwar tazara tsakanin iyakar yankin na Gaza da Isra’ila.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI