An haifi Kamala Haris ranar 20 ga watan Octoban 1964 a garin Oakland na California daga cikin tsatson bakaken Idiyawa da kuma Jamaica.
Harris ta kammala karatunta a jami’ar Howard da jami’ar California da kuma kwalejin shari’a ta Hastings inda ta zama kwarariyar lauya kuma ta fara aiki a kotun yankin Alameda.
A shekarar 2003 ne Kamala Harris ta tsunduma harkar siyasa, inda ta rike mukamai da dama da suka hadar da Karamar Sanata, Antoni Janar, inda kuma daga karshe ta zama mataimakiyar shugaba Joe Biden daga shekarar 2021 zuwa yanzu.
Kamala ce macen da tafi kowacce mace rike mukami mafi kololuwa a Amurka, na mataimakin shugaban kasa, yayinda a yanzu take takarar shugabancin kasar dungurungum.
Manya-manyan Manufofin Kamala Harris sun hadar da karfafa tattalin arzikin Amurka, fadada hanyoyin shigar Haraji,yaki da dokar haramta zubar da ciki, samar da dokoki masu tsari kan bakin haure, sauya fasalin rawar da Amurka ke takawa a Yakin Ukraine da Rahsa, da kuma alakarsa da kungiyar tsaro ta Nato hadi da yakin Gaza da Isra’ila, kyautata tsarin kiwon lafiya, saukaka hanyoyin samun kiwon lafiya musamman ga bakaken fata, kyautata tsarin dokar haramta mallakar bindiga ga fararen hula da kuma taka muhimmiyar rawa a yaki da sauyin yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI