Taƙaitaccen tarihi da manufofin Donald Trump na jam'iyyar Republican

Taƙaitaccen tarihi da manufofin Donald Trump na jam'iyyar Republican

Donald Trump tsohon shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin kasar ta Amurka an haifeshi ne a ranar 14 ga watan yunin shekarar 1946 wanda a cikin gwagwarmayarsa ta rayuwa ya kasance ɗan siyasa kuma ma’aikacin jarida sannan kuma fitaccen ɗan kasuwa.

Trump dai shine shugaban Amurka na 45 daga shekara ta 2017 zuwa 2021.

Ya kuma kammala karatunsa na digiri ne a fannin tattalin arziki a jami’ar Pennsylvania a shekarar 1968, a yayin da mahaifinsa ya sanya shi shugaban harkokin kamfanin dillancin gidajensa a 11971.

Daga bisani Trump ya sauyawa kamfanin suna zuwa Trump Organisation kuma ya sake mayar da kamfanin na ginawa da sabunta manyan gine-gine, otal-otal, gidajen caca, da wasannin golf.

Trump ya lashe zaben shugaban kasa na 2016 a matsayin dan takarar jam'iyyar Republican da 'yar takarar jam'iyyar Democrat Hillary Clinton yayin da ya rasa kuri'un da aka kada.

A yayin da Binciken Mueller ya tabbatar da cewa Rasha ta sanya masa hanu a zaben 2016 bisa nuna goyon baya a gareshi.

Donald Trump na daga cikin shugabannin Amurka da basu da gogewa a bangaren soja wanda aka danganta yawancin maganganunsa da ayyukansa da zargin wariyar launin fata da rahsin ƙaunar baƙi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)