Taƙaddama ta sanya kungiyar kasashen turai EU watsi da sakamakon zaben Venezuela

Taƙaddama ta sanya kungiyar kasashen turai EU watsi da sakamakon zaben Venezuela

Masu adawa da shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro sun hallara don zanga-zangar da shugabar 'yan adawa Maria Corina Machado ta kira kan sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi ta takaddama a kai, a birnin Caracas a ranar 3 ga Agusta, 2024.

A wata Sanarwar da Majalisar Tarayyar Turai ta fitar a jiya Lahadi ta ce ba za ta amince da sakamakon da Majalisar Zabe ta Venezuela ta gabatar a ranar 2 ga watan Agusta ba.

Hukumar zaben Venezuelan dai ta ce a zaben na ranar 28 ga watan Yuli shugaba Maduro ne ya lashe zaben, sakamakon da ya ki amincewa da zaben da aka yi tun kafin yanzu da kuma zanga-zangar da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka ce ya zuwa yanzu mutane 11 ne suka mutu, sannan aka kama wasu dubbai.

Yawancin kasashe da suka hada da Amurka da Argentina sun bayyana cewa babban dan takarar adawar kasar Edmundo Gonzalez Urrutia ne ya lashe zaben.

Kasashen Tarayyar Turai da suka hada da Faransa da Jamus da Italiya da kuma Spain na daga cikin wadanda ke neman ganin an samu gaskiya da adalci a zaben, yayin da suka yi kira ga hukumomi dake da ruwa da tsakin a harkar zaben da su fitar da cikakkun bayanai na adadin kuri’un da aka kada akasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)