Swizalan ba ta hana 'yan kasarta zuwa Turkiyya ba

Swizalan ba ta hana 'yan kasarta zuwa Turkiyya ba

Gwamnatin Tarayyar Swizalan ta bayyana kasashen waje 29 da ta ce kar 'yan kasarta su ziyarta inda babu Turkiyya a jerin sunayen kasashen.

A matakin da gwamnatin tarayyar ta dauka a ranar Alhamis din nan da ta saka dokar, ta sanya kebe kai na kwanaki 10 ga duk wadanda suka dawo daga wadannan kasashe.

Babu Turkiyya a jerin sunayen kasashen da suka hada da Amurka, Barazil, Rasha da Swidin.

Haka zalika a jerin sunayen akwai kasashe kamar su Saudiyya, Katar, Azabaijan, Armeniya, Sabiya, Iraki, Isra'ila, Chile da Peru.

Dokar hana shiga Swizalan za ta ci gaba da aiki har nan da 20 ga watan Yuli, daga sannan kuma ana sa ran kasar za ta fara aiki da dokokin Tarayyar Turai.


News Source:   www.trt.net.tr