Soylu ya mayar da martani kan yadda Girka ke muzantawa masu neman mafaka

Soylu ya mayar da martani kan yadda Girka ke muzantawa masu neman mafaka

Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya Suleyman Soylu ya mayar da martani kan yadda Girka ke muzantawa tare da zaluntar masu neman mafaka.

Soylu ya fitar da hotuna da bidiyon irin cin zarafin da aka yi wa masu neman mafaka a tekun Maliya, inda ya kuma aike da sako ga Kwamishin Harkokin Cikin Gida na Tarayyar Turai, Ylva Johansson.

A sakon nasa, Soylu ya bayyana cewa, 'yan gudun hijira 3 daga cikin 5 sun mutu bayan da jami'an tsaron tekun Girka suka yi musu duka sannan suka tura su ruwan Turkiyya a jirgin ruwan roba wanda ya nutse.

Ya ce "Ylva Johansson, zalunci da mummunan mu'amalar da Girka ke nunawa ta koma aika manyan laifuka. Shin ba za a tuhumi Girka kan wannan kisa da ta ke yi ba wanda FONTEX suka kawar da kai daga wajen?

A sakon da Soylu ya fitar cikin yarukan Turkanci da Turanci ya makala shafukan Twitter na Tarayyar Turai da FRONTEX.


News Source:   ()