Somaliya ta kalubalanci harin da Kenya ta kai kasarta

Somaliya ta kalubalanci harin da Kenya ta kai kasarta

Somaliya ta sanar da cewa harin da Kenya ta kai wa lardin Jubaland ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkata fararen hula.

A cikin bayanin da Ma'aikatar Harkokin Wajen Somaliya ta yi, an tunatar da cewa Dakarun tsaron Kenya sun kai hari ta sama ba tare da kula da farar hula ba a yankunan El-Adde da Hisa-ugur da ke lardin a ranar 3 ga Yuni.

Sanarwar ta bayyana cewa hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwa da jikkata fararen hula.

A cikin sanarwar, an lura cewa farmakan da sojojin Kenya suka gudanar da sunan yaki da tsattsauran ra'ayi bai dace da dokokin kasa da kasa ba.

Haka kuma ayayin da aka yi Allah wadai da Kenya, za a gabatar da wannan taiasar ga Ofishin Tarayyar Afırka dake Somaliyan domin hukunta wadanda ke da hannu a lamarin.

A ranar 15 ga watan Disambar shekarar 2020, Somalia ta katse duk wata huldar diflomasiyya da makwabciyarta Kenya, wacce take zargi da tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta da kuma keta mutuncin yankinta.

Alaka tsakanin Kenya da Somalia ta tabarbare bayan rikicin kan iyaka na teku a yankin mai arzikin mai da iskar gas a tekun Indiya.

Gwamnatin Mogadishu ta kuma zargi Kenya da tsoma baki a cikin harkokin siyasa a wasu jihohi, kamar Jubaland a Somalia.


News Source:   ()