Somalia da Habasha sun kama hanyar warware rikicin da ke tsakaninsu

Somalia da Habasha sun kama hanyar warware rikicin da ke tsakaninsu

Jagororin ƙasashen biyu sun ce sun cimma matsayar laluɓo masalaha bayan tattaunawar da su ka yi, wadda shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya shirya.

Shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamud ya ce a shirye ya ke ya yi aiki da Habasha, a yayin da firaminista, Abiy Ahmed ya yi na’am da ƙoƙarin Turkiyya na warware rikicin.

A wata sanarwa ta haɗin gwiwa a ranar Laraba, Somalia da Habasha sun bayyana aniyar fara tattaunawa a ƙarshen watan Fabrairu, su kuma ƙarƙare cikin watanni huɗu.

Wannan ganawar da su ka  yi ita ce ta farko tun bayan watan Janairu, lokacin da Habasha ta ce za ta gina tashar ruwa a yankin Somaliland, wanda ya ɓalle daga Somalia, inda ita kuma za ta amince da kasancewarta ƴantacciyar  ƙasa a matsayin tukuici.

Somalia ta ce ba za ta saɓu ba, tana mai watsi da yarejeniyar, tare da yin barazanar korar dakarun Habasha da aka jibge a ƙasarta don yaki da ƴan ta’adda masu iƙirarin jihadi.

Somalia ta na adawa da ƴancin kan Somaliland, wadda ta fara cin gashin kanta tun a shekarar 1991, kuma ta zauna lafiya tun daga wannan lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)