Ma’aikatar tsaron kasar Turkiyya ta sanar da cewa sojojin kasar sun baiwa awakin dutsen garin Hakkari dake kudu maso gabashin kasar harawa kasancewar rashin abincin dabbobi da yankin ke fama dashi sanadiyar zubar dusar kankara.
Sanarwar ta bayyana cewa,
"Dakarun kasarmu da suka fahinci awakin dutse na fama da tsananin yunwa, sanadiyar rashin samun abinci sakamakon zubar dusar kankara musanman a yankunan dutsen Sumbul dake karkashin gundumar Hakkari sun zubu musu da abinci iri daban daban daga jirgin saman da suke ciki”