Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ta yada wani bidiyon dake nuna yadda dakarun Turkiyya dana Azerbaijan ke atasaye mai taken Mikiyar TurAz.
Ma'aikatar ta kara da cewa dakarun Turkiyya dana Azerbaijan na ci gaba da gudanar da atasayen hadin gwiwa cikin nasara kamar yadda suka shirya.
A bidiyon anga motocin yakin sojojin Turkiyya da na Azerbaijan da kuma sojojin kasashen biyu suna zagaye.