Rundunar sojin Syria ce ta sanar da fara kai jerin hare-haren kan ‘yan tawaye a arewaci da kudancin lardin Hama, ta hanyar amfani da makamai masu linzami, da na atilary, tare da taimakon jiragen yaƙi ƙasar da na Rasha.
Sai dai a yayin da sojojin Syria ke ƙoƙarin fatattakar ‘yan tawaye daga Hama, a can lardin Homs kuwa, bayanai sun ce, dubun dubatar mutane ne suka tsare daga muhallansu saboda tunkarar lardin gadan gadan da mayaƙan ‘yan tawayen ke yi da zummar ƙwace iko da shi.
Rincaɓewar rikicin na Syria dai ya raba mutane aƙalla dubu 280 da muhallansu, tun bayan da ‘yan tawaye suka fara ƙaddamar da farmakin bazata kan sojojin Syria a ranar 27 ga Nuwamba zuwa yanzu, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.
A gobe Asabar ne kuma ake sa ran ganawa tsakanin ministocin harkokin wajen Turkiya, da Rasha da kuma Iran a Qatar, dangane da rikicin na Syria dake neman sake ƙazancewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI