Sojojin Siriya sun kai hari yankin Idlib

Sojojin Siriya sun kai hari yankin Idlib

Fararen hula 5 sun mutu, wasu 4 sun samu raunuka sakamakon harin da dakarun gwamnatin Asad ta Siriya suka kai a yankin Idlib da aka haramta rikici a cikinsa.

Sojojin gwamnati da aka jibge a gundumar Maarratunnuman da ke gudu maso-gabashin Idlib da dakarun kasashen waje da Iran ta kawo kasar ne suka kai hari ta sama da kasa a kauyen Masshun.

Bayanan da aka samu daga Kungiyar Kare Fararen Hula sun bayyana cewa, sakamakon harin fararen hula 5 da suka hada da yara kanana 4 sun mutu, an kuma jikkata wasu 5 da aka kai su asibiti.

 


News Source:   ()