Sojojin Siriya sun kai hari a yankin Bab

Sojojin Siriya sun kai hari a yankin Bab

Mutane 2 sun rasa rayukansu, wasu 5 sun samu raunuka sakamakon harin da sojojin gwamnatin Siriya karkashin Bashar Al-Asad suka kai a yankin Bab da ke arewacin kasar.

Dakarun na Asad sun kai hari da makami mai linzami kan Mayakan Kasa na Siriya da ke yankin Abu Zindin na Bab inda a watan Fabrairun 2017 Dakarun Turkiyya suka fatattaki 'yan ta'addar Daesh daga cikinsa.

Dakarun Kasa na Siriya 2 sun mutu, wasu sun samu raunuka sakamakon harin.

An kai wadanda suka jikkata zuw asibitin yankin.

 

 


News Source:   ()