Sojojin Korea ta Arewa dubu 8 na shirin yaƙar Ukraine - MDD

Sojojin Korea ta Arewa dubu 8 na shirin yaƙar Ukraine - MDD

Kawo yanzu mahukuntan Moscow ba su ce uffam ba dangane da wannan batu.

Robert Wood, shi ne mataimakin wakilin Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya, ga kuma abin da yake cewa:

Jiya mun samu labari kan damuwar da ƙasashen duniya suka shiga game da take-taken Rasha na amfani da sojojin DPRK don fafatawa da dakarun Ukraine. Muna gargaɗin Rasha kar ta kuskura ta ɗauki matakin nan mai cike da hatsari. Gudunmawar  sojojin Korea ta Arewa a yaƙi da Ukraine za ta faɗaɗa tashin hankalin da ake fama da shi.

Babban jami'in ya ƙara da cewa, sun samu wasu bayanai da ke nuna cewa, akwai sojojin Korea ta Arewa dubu 8 da aka girke su a yankin Kursk, yayin da ya miƙa wata tambaya cikin mutuntawa ga abokin aikisa na Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya ce ko shin har yanzu Rasha za ta tabbatar da  cewa akwai sojojin DPRK a Rashar? 

Amurka ta sahalewa Ukraine amfani da dukkanin makamanta masu haɗari kan Rasha

Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta ce yanzu Ukraine ba ta da wani shinge ko shamaki game da amfani da nau’ikan makamai masu haɗari da ƙasar ta bata wajen kaiwa Rasha farmaki da su, a yaƙin fiye da shekaru 2 da ɓangarorin biyu ke gwabzawa da juna.

A cewar Pentagon idan har ya tabbata cewa, Sojin Korea ta arewa sun fara taimakawa Rasha a yaƙin nata, to babu dalilin da zai kange Ukraine daga amfani da dukkanin makaman da Amurka ta bata.

Sanarwar ta Pentagon na zuwa a dai dai lokacin da ƙungiyar tsaro ta NATO ke cewa ko shakka babu Rasha ta girke dakarun na Korea ta Arewa a yankin Kursk waɗanda za su gwabza yaƙi da sojin Ukraine.

Ƙasashen yammaci na fargabar cewa girke dakarun Korea ta Arewa a Rasha kai tsaye zai faɗaɗa yaƙin duk kuwa da yadda yanzu hankali ya karkata kacokan kan rikicin Gabas ta Tsakiya.

Sakatare Janar na ƙungiyar NATO Mark Rutte ya bayyana cewa girke dakarun na Korea ta Arewa manuniya ce kan yadda Rasha ta ƙagu matuƙa wajen ganin ta samu nasara akan Ukraine da kuma yadda ta ke fatan ganin yaƙin ya ci gaba da tafiyar hawainiya ba tare da hawa teburin sulhu ba.

Mark Rutte ya bayyana cewa sabon ƙawance tsakanin Rasha da Korea ta arewa barazana ce ba kaɗai ga tsaron Turai ba har ma da tsaron gabashin Turai da nahiyar Asiya baki ɗaya.

Shugaba Joe Biden na Amurkan ya bayyana cewa matakin Rasha na gayyato sojojin Korea ta Arewa yunƙuri ne mai haɗarin gaske.

Aƙalla Sojojin Korea ta Arewa dubu 10 Amurka ke hasashen cewa sun isa Rasha yanzu haka don fafatawa a yaƙin ƙasar da Rasha.

A cewar Pentagon yanzu haka dakarun na karɓar atisaye a gabashin Ukraine ciki har da wasu ƙarin dubu 3 da suka isa ƙasar a Larabar nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)