Korea ta Arewa ta aike da dubban sojojinta domin ƙarfafa dakarun Rasha da ke yaƙi da Ukraine.
Shugaba Zelensky na Ukraine ya rubuta a shafinsa na X cewa, wasu alkaluman farko-farko da aka tattara sun nuna cewa, sama da sojojin Korea ta Arewa dubu 3 sun mutu, wasu kuma sun jikkata a yankin Kursk.
Gabanin wannan sakon na Zelensky da ya wallafa, ƙasar Korea ta Kudu ce ta fara faɗin cewa, sama da sojojin Korea ta Arewa dubu 1 ne aka kashe ko kuma jikkata tun bayan shigarsu yaƙin a cikin wannan wata na Disamba.
Shugaban na Ukraine ya ce, ya samu rahoto ne daga kwamandan rundunar sojinsa, Oleksandr Syrsky da ke sanar da shi halin da ake ciki a can filin-daga a yankin Kursk.
Kwamandan ya yi gargaɗin cewa, akwai yiwuwar Korea ta Arewa ta sake tiltilo dakarun sojinta haɗe da ƙarin makamai don ci gaba da agaza wa Rasha a wannan yaƙin.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Korea ta Arewa da Rasha ba su ce uffam ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI