Sojojin Isra'ila sun jikkata Falasdinawa 5 a Yammacin Gabar Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun jikkata Falasdinawa 5 a Yammacin Gabar Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun harbi wasu Falasdinawa 5 tare da jikkata su a lokacin da suka taru a Yammacin Gabar Kogin Jordan don gudanar da zanga-zangar adawa da mamaye yankunansu ba bisa ka'ida ba da Yahudawa ke yi.

Jami'in Kungiyar Boren Falasdinawa ta unguwar Kafr Kaddum Murad Ishtiwi ya shaida cewar, Falasdinawa sun taru tare da gudanar da zanga-zanga a unguwar Kafr Kuddum na garin Nablus da ke Yammacin Kogin Jordan.

Falasdinawan na zanga-zangar adawa da mamayar yankunansu da Yahuudawan Isra'ila ke yi.

Ishtiwi ya kara da cewar sojojinna Isra'ila sun lahanta Falasdinawa da yawa sakamakon harba musu hayaki mai sa hawaye.


News Source:   www.trt.net.tr