Sojojin Isra'ila sun jikkata Falasdinawa 2

Sojojin Isra'ila sun jikkata Falasdinawa 2

Sojojin Isra'ila sun jikkata Falasdinawa 2 a Yammacin Gabar Kogin Jordan a lokacin da suke zanga-zangar la'antar mamayar yankunansu da Yahudawa ke yi.

Majiyoyin yankin sun ce bayan Sallar Juma'a ne Falasdinawa suka gudanar da zanga-zangar la'antar matakin mamayar yankunan Asira, Kalkiya, Kafr Kaddum da Al-Halil da ke garin nablus da Yahudawan Isra'ila ke yi.

Sojojin Isra'ila sun yi amfani da harsashan roba wajen jikkata masu zanga-zangar.

A yankin Asir Falasdinawa 2 sun jikkata.


News Source:   www.trt.net.tr