An gudanar da zanga-zangar adawa da matsugunan yahudawa ba bisa ka'ida ba a Yammacin Gabar Kogin Jordan. Falasdinawa 93 ne suka jikkata sakamakon shiga tsakani da sojojin Isra’ila suka yi a cikin zanga-zangar.
Falasdinawa sun gudanar da zanga-zangar adawa da matsugunan yahudawa ba bisa ka’ida ba a sassa daban-daban na Yammacin Kogin Jordan, musamman a garin Bayta da ke Nablus da garin Kefr Kaddum da ke lardin Kalkylya.
Sojojin Isra'ila sun mayar da martani ga masu zanga-zangar da hayaki mai sa hawaye da kuma harsasai na gaske da na roba. Falasdinawan sun mayar da martani ta hanyar jifar sojojin da duwatsu.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa daga kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Falasdinu, an bayyana cewa Falasdinawa 93 sun ji rauni, 23 daga cikinsu na gaske kuma 70 daga cikinsu harsasai na roba, a yayin shiga tsakani na sojojin Isra'ila.
A cikin sanarwar, an kuma bayyana cewa, a cikin wadanda suka samu rauni sakamakon harsasai na roba, akwai wani ma'aikacin kiwon lafiya da ke aikin jin kai a Red Crescent na Falasdinu.
An bayyana cewa, masu zanga-zangar da yawa sun shafu da hayaki mai sa hawaye da aka harba kalubalantar da sojojin Isra'ila suka yiwa masu zanga-zangar.
Akwai matsugunan yahudawa sama da 250 ba bisa doka ba a Yammacin Gabar Kogin, wanda Isra'ila ta mamaye a shekarar 1967. Fiye da yahudawa 'yan share wuri zauna dubu 450,000 da ke zaune a wadannan wurare sun kara wahalar da rayuwar Falasdinawa da ke rayuwa karkashin mamaya a Yammacin Gabar Kogin.
A karkashin dokar kasa da kasa, ana daukar duk matsugunan yahudawa a yankin Falasdinawa a matsayar yankunan da suka mamaye.