Sojojin Isra'ila sun raunata Falasdinawa 108 a zanga-zangar adawa da matsugunan yahudawa ba bisa ka'ida ba a Yammacin Gabar Kogin Jordan.
Falasdinawa sun gudanar da zanga-zangar adawa da mamayar yahudawa 'yan mamaya suke yi a yankuna daban-daban na Yammacin Gabar Kogin da ta mamaye.
Sojojin Isra’ila sun kalubalanci masu zanga-zangar da harsasan roba da hayaki mai sa hawaye.
A sakamakon wannan tsaka mai wuya, Falasdinawa 108 sun ji rauni, 68 daga cikinsu da harsasai na roba, kuma hayaki mai sanya hawaye da sojojin suka yi amfani dashi ya taba wasu.
Daga cikin wadanda suka jikkata har da masu daukar hoto 2, daya daga cikinsu dan jarida ne mai zaman kansa wanda ke aiki da kamfanin dillancin labaran Anadolu (AA), Nidal Istiye. Wani dan jarida mai daukar hoto na AA mai zaman kansa ya ce sojojin Isra’ila kai tsaye suka auna wa ‘yan jaridar da harsasai na roba, kuma harsasai 3 suka same kafarsa ta hagu.
'Yan mamayar yahudawa fararen hula suna kokarin kafa kananan sansani na ayari da gidajen kwantena a wurare da dama na Falasdinu. An kara wasu gine-ginen a wadannan sansanonin daga baya, lamarin dake kara bayyanar da mamayar da Israilawan keyi.
Sama da Yahudawa dubu 450,000 ne suka mamaye wasu yankunan Falasdinu, wacce Isra’ila ta mamaye a shekarar 1967.