An bayyana cewa, sojojin Isra'ila sun boye yadda suka kashe fararen hula 6 a yayin kai hare-hare a Zirin Gaza a watan Mayu.
Jaridar Haaretz da ke Isra'ila ta bayar da labarin cewa, a ranar 13 ga Mayu duk da an yi shirin yin ruwan bama-bamai a Bayt Hanun amma ba a gargadi jama'ar yankunan da su bar gidajensu ba.
A yayin kai hare-haren fararen hula 6 da suka hada da mata 3, yara kanana 2 da namiji babba 1 sun mutu. An kuma jikkata wasu fararen hular 25.
An bayyana cewa, sojoji sun gudanar da bincike game da lamarin amma ba a bayyanawa jama'a sakamakonsa ba, an kuma dakatar da wasu kananan sojoji amma daga baya aka mayar da su abkin aiki.
Haka zalika an bayyana babu wani soja da aka hukunta sakamakon lamarin.